Iran Ta Gargadi Kasar Saudiya Game Da Makircin Da Amurka Da Isra’ila Suka Kullawa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasar saudiya  game da makircin da  Amurka da Isra’ila suka kitsawa na kai hare –hare a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasar saudiya  game da makircin da  Amurka da Isra’ila suka kitsawa na kai hare –hare a yankin, kuma ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho tare da ministan harkokin wajen saudiya faisal bin Farhan a jiya Asabar

Ministan ya kara da cewa duk wani matakin kai hari da Amurka ko isra’ila za su dauka kan kasar iran ko kuma taimakawa ko yin aiki tare da wata kasa za ta yi kan wannan mataki to ko shakka babu zai gamu da mayar da martani mai tsanin daga dakarun kare juyin musulunci na kasar iran

Yace Iran kasar Amurka tana ci gaba da kaddamar da hari kan kasar iran bayan ta keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin iran da Amurka,  da kasar Pakistan ta shiga tsakanin, wanda hare-haren yake amfanin da sauran kasashen dake taimaka mata a yankin, sai dai tuni dakarun sojin kasar iran suka mayar da martani kan muradu Amurka dake yankin

Tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen iran da na saudiya yana zuwa ne adaidai lokacin da Washington ke ci gaba da dagewa kan kudurinta na take hakki da kuma kokarin fadada yaduwar yaki tare da hadin guiwar kasashe masu tasiri a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted