Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta gargadi Amurka akan ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwanta.
Hedikwatar Sojojin Iran na Tsakiya ya yi gargadin cewa “ci gaba da toshe hanyoyi da ayyukan fashin teku ” da sojojin Amurka ke yi a yankin zai haifar da martani mai tsauri daga sojojin Iran.
” Hedikwatar ta jaddada cewa sojojin Iran yanzu na da ” karfi ” don kare ‘yancin kasar, da muradun kasa.
Sanarwar ta sake nanata kudurin kasar na sa ido kan motsin abokan gaba a yankin da kuma ci gaba da cikakken iko a kan mashigin teku na Hormuz.
Hukumomin Iran sun dage cewa wannan toshewar haramtacciyar hanya ce kuma ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta matakai biyu da ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu kuma shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita ta ba tare da bata lokaci ba ‘yan sa’o’i kadan kafin cikar wa’adinta a ranar 22 ga Afrilu.
Iran ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani zaman tattaunawa ba a karkashin mastin lamba ko tilastawa ba.