Iran ta gargadi Amurka akan ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwanta

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta gargadi Amurka akan ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwanta. Hedikwatar Sojojin Iran na Tsakiya ya yi gargadin cewa “ci gaba da toshe hanyoyi da ayyukan fashin teku ” da sojojin Amurka ke yi a yankin zai haifar da martani mai tsauri daga sojojin Iran. ” Hedikwatar ta jaddada cewa […]

Amurka : An fitar da Trump daga dakin liyafa bayan harin bindiga

A Amurka an fara aza ayar tambaya game da batun tsaro ga mayan jami’an tsaron kasar bayan harin da wani dan bindiga ya kai a wajen liyafa da ‘yan jarida a birnin Washigton. An kai harin ne a wajen liyafar cin abincin dare na shekara-shekara na kungiyar ‘Yan Jarida ta Fadar White House a Otel […]

Iran : Araghchi na ran-gadi a kasashen Pakistan, Oman da Rasha

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Abass Araghchi, ya fa wani ran gadin aiki a kasashen Pakistan, Oman da kuma Turkiyya. Mista Araghchi ya isa birnin Islamabad na Pakistan a ranar Juma’a da yamma. Ya tattauna da mahukuntan Pakistan kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen, halin da ake ciki a yankin da […]

Mali : Sojoji sun murkushe harin ta’addanci a Sansanonin Sojoji da dama

Sojojin Mali sun sanar da cewa “kungiyoyin ‘yan ta’adda ” sun kai hari kan wurare da sansanonin sojojin kasar da dama ciki har da Bamako, Kati, Gao, Kidal, Sévaré. Hukumomi sunyi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu da kuma taka tsantsan. Rundunar Sojin Mali (FAMa) ta sanar cewa ta dakile yunkurin kai hare-hare […]