Iran Ta Gabatar Da Shawarar Da Zata Kawo Karshen Yakin Da Ake Yi Da Ita

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sun gabatar da shawara don kawo karshen yakin, kuma yanzu haka dabara ta rage wa Amurka Kazem

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sun gabatar da shawara don kawo karshen yakin, kuma yanzu haka dabara ta rage wa Amurka

Kazem Gharibabadi, Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran kan harkokin Shari’a da Harkokin Ƙasashen Waje, ya sanar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da shawara ta ƙarshe don kawo ƙarshen yaƙin da aka ƙaƙaba mata, yana mai jaddada cewa, yanzu haka zabi yana hannun Amurka don yanke hukuncin karshe.

A cikin jawabinsa, Gharibabadi ya bayyana cewa: Shawarar Iran tana da nufin kawo ƙarshen hare-haren wuce gona da irin da Amurka da ‘yan Sahayoniyya ke kaiwa Iran, yayin da a lokaci guda take tabbatar da cikakken shirin Jamhuriyar Musulunci na tunkarar duk wani hari da kuma kare ikonta da al’ummarta.

Jami’in na Iran ya jaddada cewa: Iran koda yaushe tana bin ƙa’idodin diflomasiyya bisa ga cimma muradun ƙasa da kuma warware matsalolin da suka kunno kai.

Gharibabadi ya tabbatar da cewa: Iran ta shirya tsaf don tabbatar da tsaron ƙasa da muhimman muradunta, yana mai jaddada cewa, wannan shiri ba ya karya ƙa’idodin Iran na rashin amincewa da Amurka da kuma jajircewarta ga gaskiya da bayyana gaskiya a cikin tsarin diflomasiyya.

Ya kamata a lura cewa waɗannan ci gaban sun biyo bayan wani muhimmin taro na ƙasashe uku da jakadun China da Rasha suka yi da Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Shari’a da Harkokin Ƙasashen Duniya, wanda ke nuna muhimmancin shawarwarin ƙasashen duniya kan hanyoyin magance rikicin da ake ciki a yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted