Iran ta ce tana nazarin amsar da Amurka ta gabatar mata ta hanyar Pakistan

Iran ta ce tana nazarin amsar da Amurka ta gabatar mata a game da shawarwarin nan guda 14 da ta mika ta hanyar masu shiga

Iran ta ce tana nazarin amsar da Amurka ta gabatar mata a game da shawarwarin nan guda 14 da ta mika ta hanyar masu shiga tsakani na Pakistan.

“Amurkawa sun ba da amsarsu ga shirin da muka gabatar ta hanyar bangaren Pakistan, kuma a halin yanzu muna duba su,” in ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmaeil Baghaei.

Ya fayyace cewa shawarar Iran ta mayar da hankali ne kawai kan kawo karshen yakin Amurka da Isra’ila kan Iran da kuma tashin hankali a yankin amma babu wani tanadi da ya shafi batun shirin nukiliya na kasar” in ji Baghaei.

Ya yi watsi da rahotannin da aka samu kwanan nan, musamman daga tashar talabijin ta Al Jazeera, wanda ya yi ikirarin cewa shirin mai maki 14 ya kunshi dakatar da ayyukan nukiliya na Iran na tsawon shekaru 15 da kuma yiwuwar hadin gwiwar Amurka da Iran kan ayyukan share nakiyoyi a mashigin Hormuz.

Ya nuna cewa batutuwan nukiliya da aka tabo kwanan nan an tattauna su a tattaunawar da ta gabata tsakanin Tehran da Washington kuma ba su da alaka da shirin na yanzu.

Amurka da Isra’ila sun kaddamar da yaki kan Iran a tsakiyar watan Yuni da kuma karshen watan Fabrairu yayin da Tehran ke tsakiyar tattaunawar diflomasiyya da Washington kan shirin nukiliyarta na zaman lafiya, in ji shi.

“A halin yanzu ba mu shiga wata tattaunawa kan batun nukiliya ba, kuma za a yanke shawara game da makomar nan gaba,” in ji shi.

Iran dai na mai nanata cewa ba ta yarda da tattaunawa a karkashin mastin lamba ko gindaya mata wa’adi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted