Iran Ta Ce: Taken Yaudarar Amurka Da Na Yammacin Turai Ya Kawo Karshe A Idon Duniya

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Taken abin dariya da shugabannin yammacin duniya ke maimaitawa shi ne taken kare hakkin dan adam Kakakin ma’aikatar

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Taken abin dariya da shugabannin yammacin duniya ke maimaitawa shi ne taken kare hakkin dan adam

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: A yanzu haka fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila mai aikata laifukan ta’addanci yana wajen uwar gijiyarsa, watanni tara bayan ya aikata kisan kiyashi tare da kashe kananan yara da mata. Kan’ani yana mai jaddada cewa; Taken mafi ban dariya da take fitowa daga bakunan shugabannin Amurka da na yammacin Turai shi ne taken karyar kare hakkin dan adam.

Kan’ani ya kara da jaddada cewa: Fira Minista mai laifi na haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya yau kusan watanni goma sha biyu yana aikata kisan kiyashi da kashe yara da mata, a yau yana karkashin liyafar uwar gijiyarsa Amurka, don haka ƙoƙarin yaudara na wayewar yammacin duniya da ake ta yadawa cikin shekarun da suka gabata don nuna fuska marar laifi da mutuntaka ga duniya, yaudarar ta kawo karshe, kuma labulen da suke sanyawa wajen rufe fuskarsu ta hakika ya yaye, kuma mummunar dabi’a da rashin tausayi na manufofin Amurka sun bayyana ga duniya gaban duniya.

Kan’ani ya jaddada cewa: Taken da ya fi fitowa daga shugabannin Amurka da na Turai shi ne taken kare hakkin bil’ Adama. ‘Yancin Falasdinawa da suka hada da ‘yancin rayuwa da samun tsaro da samun ruwa da abinci da magunguna da sauransu an yi fatali da su a Zirin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan ta mafi munin hanyoyi a idon duniya, da kuma kashe-kashen yaran Falasdinawa a kullum rana, a hannun mahauci haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma babu wani kwakkwaran mataki da duniya ta dauka wajen dakatar da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments