Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Bakae ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani ma’aikacin hukumar makamashin nukliya ta duniya a cikin kasar. Kuma al-amarin yadda iran zata yi hulda da hukumar bayan yakin kwanaki 12 ya koma hannun majalisar dokokin kasar da kuma majalisar koli ta harkokin tsaron kasar.
Kakakin ya kara da cewa daga yanzu mu’amala da hukumar ta IAEA dole ne ta kasance ta yadda Iran zata kare amincin cibiyoyin makamashin nuliya ta kasar. Da kuma tabbatar da cewa babu wata sirrin kasar wanda zai isa hannun makiyanta.