Gwamnatin Tehran ta yi Allah wadai da harin Amurka kan tashoshin na’urorin radar na kasar, inda ta kira shi da keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Afrilu da kuma sake tabbatar da halalcinta na kare kai.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki mataki kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ke yi akai-akai.
Hare-haren da Amurka ta kai kan tashohin na’urorin radar da na sa ido a bakin teku a yankin kudancin Sirik da kuma tsibirin Qeshm ya zama “keta doka” ga yarjejeniyar tsagaita wutar da kuma hurumin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta kare ikonta, tsaronta, da muradun kasa da dukkan karfinta.
Ma’aikatar ta kuma yi kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kwamitin Tsaro, da sauran hukumomin kasa da kasa masu alhakin daukar mataki cikin gaggawa da inganci ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ke ci gaba da yi da ayyukanta ba bisa ka’ida ba, da kuma ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da kasa da kasa.”
Wannan sanarwar ta biyo bayan wani sako da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafinta na X, wanda ke nuna cewa ta dakile jiragen sama marasa matuki guda hudu na Iran da aka harba zuwa mashigin Hormuz, tana mai ikirarin cewa wadannan jiragen marasa matuki suna barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa na yankin, kuma daga baya sojojin Amurka suka kai hari kan wuraren radar na sa ido kan gabar tekun Iran a Goruk da kuma tsibirin Qeshm domin kare kansu daga hare-hare.