Kasar iran ta taya alumma da gwamnatin kasar iraki farincikin ficewar sojojin mamayar Amurka da sauran sojojin mamaya daga kasarsu bayan kwashe gomiya biyu suna zaune a kasar, ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana ficewar sojojin Amurka daga iraki a matsayin babban mataki wajen kare martabar da kuma yanci kasar iraki,
Ma’aikatar harkokin wajen ta ce kasancewar sojojin mamayar Amurka da sauran kawayenta a iraki na tsawon shekaru 23 ya fara ne daga lokacin da Washington ta kaddamar da yaki kan kasar iraki a ranar 20 ga watan maris din shekara ta 2003 da karyar lalata makaman nukiliyar kasar
Haka zalika ta bayyana irin mummunan sakamakon da aka samu na mamayar da Amurka ta yi a iraki da ma yankin baki daya, inda aka kashe mutane sama da miliyan 1, da suka hada da dubban mata da yara kanan da basu dauki alhakin kowa ba, da kuma lalata muhimman kayayyaki da kudinsu ya kai daruruwan daloli na fararen hula da sauran muhimman gine ginen gwamnati, da kuma tafka muggan laifuka kan alummar kasar da suka hada da azabtar da maza da mata a gidan yarin Abu Guraib
Daga karshe ma’aikatar ta jinjina musu game da tsayin daka da alummar iraki suka nuna kan yan mamaya, ta’addanci, da rarrabuwar kai, kana ta jaddada cewa dole ne a mutunta cikakken ikon mallakar kasa da kuma iyakokin kasar iraki