Lebanon: Sojojin Mamaya Sun Jikkata A Kudancin Kasar Lebanon

Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun sanar da cewa biyu daga cikinsu sun jikkata sanadiyyar fashewar wani bom bisa kuskure a ranar Juma'ar da ta
sojojin mamaya

Sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun sanar da cewa biyu daga cikinsu sun jikkata sanadiyyar fashewar wani bom bisa kuskure a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sanarwar sojojin mamayar sun ce daya karamin soja ne sai kuma dayan da ofisa ne,kuma tuni an dauke su zuwa Asibiti, bayan da aka sanar da iyalansu.

Wannan lamarin dai  ya faru ne a daidai lokacin da sojojin mamayar suke ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, tare da rushe gidajen mazauna yankunan da kuma kashe wasu.

Sojojin na mamaya dai suna amfani da jiragen yaki da manyan bindigogi da su ka grike a yankin wajen kai hare-hare da lalata gonaki da gidaje.

A wani gefe,kafar watsa labaru  ta ‘yan sahayoniya “Valla” ta ce; Adadin sojojin da aka kashe daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu sun kai 1318.

A yau Lahadi kafar watsa labarun ta “Valla” ta buga rahoto akan adadin sojojin sahayoniya da aka kashe a dukkanin fagagen yaki tana mai kara da cewa alkalumman sun hada sun kuma hada da ‘yan sanda da ma’aikatan hukumar leken asirin cikin gida ta “Shabak” da masu aikin kashe gobara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted