Iran Ta Yi tir Da ‘Babban Karyat Trump Kan Magunguna A Kasar

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da ke Vienna ya musanta zancen shugaban kasar Amurka na cewa JMI tana samar da magunguna a cibiyoyin makamashin

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da ke Vienna ya musanta zancen shugaban kasar Amurka na cewa JMI tana samar da magunguna a cibiyoyin makamashin nukliya na kasar.

Kamafanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ofishin jakadancin JMI a Vienna yana maida martani wa Donal Trump kan karyar da ya fadawa masu zabe a birnin Duranta na jihar Oklohoma kan cewa JIM tana samar da magungunta tare da amfani da makamashin nukliya a cibiyoyin makamashin nukliya na kasar.

Ofishin jakadancin y ace, wannan ma babban karya ce, kamar yanda shugaban ya sha yiwa JMI karya. Sannan ya kara da cewa hukumar UNODC ta MDD mai kula da al-amuran miyagun kwayoyi da safararu ne yakamata ta yi wannan bayanin, ko ta tabbatar da hakan. Har’ila yau da kuma hukumar ‘ the International Narcotics Control Board (INCB).ne yakamata su fadi haka idan ya faru.

Shugaba Trump a taron yakin neman zabe wa jam’iyyar sa ta Republican a birnin Durant na Jihar Oklohoma, sannan yana son ya bayyana masu dalilan da sukasa ya kaiwa iran hare hare, sai yace wai suna samar da magunguna a masana’antunsu na nukliya, kuma ya bugesu sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted