Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa Amurka ta ji haushin Iran kan yanda ta fuskanceta a yakin da ta dora mata watannin kimani 7 da suka gabata, ya kuma kara da cewa, Amurka da kawayenta zasu fukantar sabbin matsaloli daga JMI idan sun ci gaba da yakarta, sannan a lokacinda Iran take yaki tana kuma ci gaba da bin hanyar diblomasiyya idan Amurka ta dawo cikin hayyacinta.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a safiyar yau lahadi ya kuma kara da cewa, a baya bayan nan Amurka ta aika sako ta masu shiga tsakani sabanin abinda ta bayyana a fili ko ta fadawa kafafen yada labarai. Ya ce wasa da hankali da samun karin lokacin shirin yaki ko kuma gabatar da bukatu na bangare guda ba zai sake amfani a kan kasar Iran ba.
Qalibaf ya sake jaddada cewa, sharuddan kasar Iran na kawo karshen yaki a fili suke, kuma ba zata sake bude mashigar ruwa ta hurmuz ba sai tare da cika sharudda 7 wadanda ta lissafa, wadanda kuma suke cikin takardar fahintar juna ta Islamabad.
Ya ce Iran yi aiki ne da abinda Amurka da kawayenta suka aikta ba surutu da kuma farfagandar da suke yadawa nan da can ba. Iran a shirye take ta fuskanci duk shirin da suka shirya saboda tana cikin karfinta na yaki ta ko ina.
Adaga karshe ya ce, karkashin jagorancin Aya. Mujtaba Khaminaei jami’an tsaro da mutanen kasar ba zasu bar Amurka ta cimma manufarta na ganin bayan JMI ba.