Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan alamuran sharia da kuma na kasa da kasa ya bayyana cewa, jawabinda gwamnatin Amurka ta bayar dangane da shawarar JMI na bude mashigar ruwa ta Hurmuz cikin kwanaki 7, yana nan ana ci gaba da bincikensa a hukumomi da suka dace.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Gharibabadi yana fadar haka a yau Lahadi a tarun addu’ar uku na wafatin yar’uwan ministan harkokin waje Malama Badar Assadati a safiyar yau Lahadi 4 ga watan Octoban shekara ta 2026.
Gharib Abadadi ya ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a ganawarsa da tokwaransa na kasar Qatar kuma daya daga cikin wadanda suke shiga tsakanin Iran da Amurka, ya gabatar masa wannan shirin kuma a makon da ya gabata ne Amurka ta bada Amsar ta hannun kasar Qatar . Kuma tun lokacin jami’an gwamnatin da abin ya shafa suna gudanar da bincike a kansa.
A cikin shawarar dai Iran ta nunawa Amurka wani tsari na kawo karshen bude mashigar ruwa ta Hurmuz tare da cika sharuddan da Iran take bukata a cikin takardan fahintar juna ta Islamabad.
Daga Karshe Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran a shirye take kan duk abinda Amurka ta zaba bayan wannan.