Aragchi Ya Ce Iran Ta Bayyanawa Duniya Tana shirin Yaki ko sulhu

Ministan harkokin wagen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana cewa, halattar tawagar JMI a taron babban zauren MDD karo na 81 ya fahintar da duniya

Ministan harkokin wagen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana cewa, halattar tawagar JMI a taron babban zauren MDD karo na 81 ya fahintar da duniya cewa kasar a shirye take ga zaman lafiya ko kuma yaki da Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Asabar a jawabin da ya gabatarwa jakadu da jami’an diblomasiyya na kasashen duniya Tehran. 

Ya kuma kara da cewa a tarpon kama daga jawabin shugaban kasa, da ganawa da sauran shuwagabannin gwamnatin na jami’an kasashen duniya daban daban da kungiyoyin kasa da kasa da yan jaridu, Iran ta bayyana matsayinta a fili.

Yace tunanin wasu Jami’an gwamnatin kasar Amurka kan cewa, za’a maida iran saniyar ware a kuma wulakantata bai auku ba. Kuma Jami’an gwamnatin JMI ta kamar yadda aka saba shiga taron har aka kammala ba tare da ta sami matsala da wata kasa ko kuma wani ya sauya mata fuska ba. Ta gana da jami’an gwamnatoci da yan jaridu daban daban na duniya da na Amurka da kum ashuwagabannin kungiyoyin kasa da kasa.

Yace wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu jami’an gwamnatin Amurka na cewa an kori tawagar kasar Iran daga taron ba gaskiya ba ne, sun je NewYork kuma duk suka dawo Iran kamar yadda aka tsara tafiyar.

Amma a taron Amurka ta nunawa duniya kan cewa bata cancanci karban bakwancin wannan babban taron ta shuwagabannin kasashen duniya ba, ta musamman irin mummunan jawabin da shugaba Trump a gabatar a ranar bude taron.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted