Sojojin gwamnatin kasar habasha sun kwace iko da birnin Meklle babban birnin yankin Tigray na kasar a jiya Asabar a dai dai lokacinda shuwagabannin kungiyar kwatar yencin mutanen Tigray suna ganawa da shuwagabbin kasashe masu adawa da Habasha a kasar Masar.
Shafin yanar gizo ta labarai Arabnews ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin Habasha ne suke iko da birnin Mekelle babban birnin yankin Tigray a jiya Asabar bayan fafatawa da mayakan TPLF masu son ballewa daga kasar na fiye da mako guda.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa, mafi yawan mayakan TPLF sun bar garin kuma tun an maida layukan wayoyi wadanda aka yanke tun lokacin kimani kwanaki 10 da suka gabata. Babu yan sanda a kan titunan birnin. Amma kuma babu yaki a cikinsa.
A dayan bangaren kuma shuwagabannin kungiyar ta TPLF suna ganawa da Abdulfattah Assisi na kasar Masar da shugaba Isaias Afwerki na kasar Eriteria sai kuma shugaba Hassan sheikh Muhammad na kasar Somalia da Abdel Fattah Al-Burhan na kasar Sudan a garin Alamein a gefen taron kasuwanci na kasashen afrika.
Shugaban kungiyar yantawayen Debretsion Gebremichael ya ce kungiyarsa zata ci gaba da yakar gwamnatin Habasha har zuwa yencin yankinsu.