Netanyahu Ya Bayyana Birtaniya A Matsayin Fandararriyar Daula

Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra'ila Benjemine Netanyahu ta bayyana Birtaniya da cewa fandararriyar Daul ace tare da zarginta da cewa tana biyewa "kungiyoyin Musulmi" wajen
fira ministan isra'ila

Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjemine Netanyahu ta bayyana Birtaniya da cewa fandararriyar Daul ace tare da zarginta da cewa tana biyewa “kungiyoyin Musulmi” wajen fada da Isra’ila.”

Netanyahu wanda jaridar “Daily Mill” ta Birtaniya ta yi hira da shi ya kuma bayyana Birtaniya da nuna halayyar munafinci tare da yi mata gorin cewa; Ta hanyar bayanan sirri da su ka ba ta, sun tserarar da rayukan ‘yan Birtaniya da kuma kasashen yammacin turai da yawa daga hare-haren ta’addanci.

Firan ministan na Birtaniya wanda kotun duniya ta manyan laifuka ta fitar da sammacin kamo shi saboda kisan kiyashi a Gaza, ya kuma ce; Birtaniya tana tafiya kafada da kafada da ‘yan ta’adda wadanda suke kai musu hari,sannan kuma suna fada da masu kare su.

A cikin kwanakin bayan nan ne dai Birtaniya ta kakaba takunkumi akan kayayyakin da ake kerawa a sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna saboda  an gina su ne sababnin kudurorin MDD.

Haka nan kuma London ta dakatar da Shirin sayar wa da Haramtacciyar Kasar ta yahudawa makamai da duk wasu kayayyaki da za su taimaka wajen ci gaba da mamaya.

Ita dai Haramtacciyar Kasar Isra’ila kirkirar Birtaniya ce a 1948 da shi ne musabbabin jefa falasdinawa cikin halin da suke ciki a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted