Gaza: Falasdinawa 9 Sun Jikkata Sanadiyyar Hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Rahotanni daga Gaza suna cewa wasu falasdinawa 9 sun jikkata daga cikinsu da karamin yaro sanadiyyar harin da waji jirgi maras matuki na 'yan sahayoniya
baraguzan gaza

Rahotanni daga Gaza suna cewa wasu falasdinawa 9 sun jikkata daga cikinsu da karamin yaro sanadiyyar harin da waji jirgi maras matuki na ‘yan sahayoniya ya kai a kudancin Deir Balah a tsakiyar zirin Gaza.

Tashar talabijin din “almayadeen” ta nakalto ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza tana tabbatar da abinda ya faru,sannan kuma ta ambato alkalumman adadin shahidai tun daga 11 ga watan Oktoba na 2025 zuwa yanzu da sun kai 1,445, wadanda su ka jikkata kuma sun kai 5,075. Bugu da kari a wannan tsakanin kungiyoyin agaji na Falasdinawa sun yi nasarar zakulo Shahidai 835 daga karkashin baraguzai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted