Iran Ta Allahwadai Da Jakadan Kasar Amurka Kan Kalamansa Dangane Da Fadada HKI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi tir da kalaman jakadan Amurka a HKI dangane da shirin fadada HKI a yankin Asia

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi tir da kalaman jakadan Amurka a HKI dangane da shirin fadada HKI a yankin Asia ta yamma. Ya kuma kara da cewa kalaman Mike Huckabee ya nuna irin yadda Amurka take da hannu dumu dumu a cikin shirin HKI na fadada mamayar da takewa kasar Falasdinu zuwa sauran kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mike Huckabee yana fadar haka a baya bayan nan, inda ya ce, yakamata HKI ta kammala aikin gaba daya, ta kuma fadada mamayar da kogin Nilu na kasar Masar zuwa kogin Furat a kasar Siriya da Iraki.

Jakadan ya kara da cewa yahudawan sahyoniya suna da hujjar mallakar wadan nan yankuna a cikin bible kuma kammala aikin yafi dacewa.

Mamayar da HKI takewa gidajen Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan a halin yanzu dai ya na dushe fatan falasdinawa na kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci a kusa da HKI kamar yadda masu ra’ayin kasashe biyu suke so.

Kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa da dama sun yi alla wadai da kalaman jakadan wanda yake bayyana irin goyon bayan da Amurka take bawa HKI a cikin ta’asar da take aikatawa a kasar Falasdinu da ta mamaye shekaru kimani n80 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted