Search
Close this search box.

Iran: Sakonnin Ta’aziyya Shahadar Ra’isi Daga Shuwagabanni Da Fitattun Mutane A Duniya Suna Isowa Kasar

Sakonni ta’aziyya daga shuwagabnni gwamnatoci da fitattun mutane da kungiyoyi na kasa da kasa suna shigawa kasar bayana shahadar shugaban kasar JMI Hujjatul Islam Ibrahim

Sakonni ta’aziyya daga shuwagabnni gwamnatoci da fitattun mutane da kungiyoyi na kasa da kasa suna shigawa kasar bayana shahadar shugaban kasar JMI Hujjatul Islam Ibrahim Ra’isi a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yana mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da mutanen kasar Iran dangane da rashin shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da tawagarsa. A cikin sakon, shugaba Putin ya bayyana Ra’isi a matsayin shugaba wanda ya bada duk abinda ya mallaka don khidima wa mutanen kasar Iran. Yace shugaban ya cancanci girmamawa daga dukkan mutanen kasar Iran saboda yadda ya bada rayuwarsa don khidimawa mutanen kasarsa.

Har’ila yau Shahbaz Sharif firai ministan kasar Pakistan ya taya mutanen kasar Iran ta’aziyar shahadar shugaba Ra’isi da wadanda suke tare das hi. Ya kuma sanya rana guda a matsayin makoki a kasar Pakistan saboda rashin shugaba Ra’isi.

Har’ila shugaban shugaban  kasar Armanistan, Sarkin Haddiyar daular Laarbawa Muhammad Bin Zaid Aalinahiyan duk sun aiko da ta’aziyyarsu dangane da shahadar shugaban.

A wani labarin kuma shugaban majalisar dokokin tarayyar Turai Charles Michel ya rubuta a shafinsa na tweeter, inda yake ta’aziyyar shahadar shugaban Ra’isi da wadanda suke tare da shi ga gwamnatin da mutanen kasar Iran. Shugaban kasar Bolivia Luwis Orse, da sarkin Qatar Tamim bin Hamda Aali Thani duk sun aiko da ta’aziyarsu na rashin shugaba Ra’isi.

A wani labarin kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta aiko da ta’aziyya ga mutanen da gwamnatin kasar Iran kan wannan rashin.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments