Search
Close this search box.

Iran: Sakon Jagora Dangane Da Shahadar Shugaba Ra’isi Da Wadanda Suke Tare Da Shi

Jagoran juyin Juya Halainb Musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamina’ii ya fidda sakon taziyya na shahadar shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da wadanda

Jagoran juyin Juya Halainb Musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khamina’ii ya fidda sakon taziyya na shahadar shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da wadanda suke tare da shi a wani hatsarin jirgin saman day a samesu a jiya da rana a lardin azarbianjan na gabas.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa ofishin jagoran ya fitar da sakon kamar haka.

Da sunan All..mai rahama mai jin kai, daga All..muke kuma gareshi muke komawa.  Na karbi sakon mai sosa raid a kuma daci, na shahadar shugaban kasa mujahid, mai khidimar Imam Ridha (a) mai girma Hujjatul Islam Ibrahim Ra’isi, da wadanda suke  tare da shi, All.. ya yarda da su gaba daya.

Jagoran ya kara da cewa: Wannan hatsarin wanda ya kai shugaban da wadanda suke tare das hi ga shahada, asarace babba ga mutanen Iran, saboda irin yadda baya gajiya wajen khidima da kuma yiwa mutane aiki. Y ace: A lokacin ayyukansa na shugaban kasa da ma kafinsa haka ya nuna cewa mutum ne mai son mutane kuma wanda yake aiki don neman yardarsu, wanda ya kasance yardarm All..na cikinsa.  Sannan ya kara da cewa a wannan hatsarin, mun rasa manya manyan mutane kamar Hujjatul Islam Aali Hashim limamin masallacin jumma’a na birnin Tabriz, da Hussain Amir Abdullahiyan ministan harkokin waje mai kokari, da Maliki Rahamati gwamnan larsin Azarbaijan ta gabas mai kishin addini da kuma tawagar matuka jirgin shugaban da wasu wadanda suke aiki tare da shi.  Daga karshe Jagoran ya shelanta makoki na kwanaki 5 a duk fadin kasar saboda girmama wadannan manya manyan jami’an gwamnatin JMI wadanda suka koma  ga rahamar Ubangijinsu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments