Iran: Rundunar IRGC  ta sanar da shahadar Shugaban Hamas Isma’ila Haniya a hukumance

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falastinawa Hamas, Isma’ila Haniya ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kaddamar a kan masaukinsa a birnin

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falastinawa Hamas, Isma’ila Haniya ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kaddamar a kan masaukinsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.

A cikin wata sanarwa wadda dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran suka fitar, sun bayyana cewa shugaban kungiyar ta Hamas Isma’ila Haniya ya yi shahada tare da daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa masaukinsa.

Sanan nan kuma rundunar da IRGC ta bayyana cewa, ta shiga gudanar da bincike kan lamarin, wanda zata sanar da sakamakonsa nan bad a jimawa ba.

Haniya ya isa birnin Tehran ne a jiya dmin halartar taron rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masud Pezeshkian, wanda a ka gudanara  jiya a majalisar dokokin kasar Iran, tare da halartar tawagogi daga kasashen duniya.

Haniya ya gana sabon shugaban kasar ta Iran a yammacin jiya Talata, inda suka tattauna kan halin da ake ciki a Gaza da kuma kisan kare dangi da Isra’ila take yi wa fararen hula a Gaza.

Baya ga haka kuma Haniya ya gana da jagoran juyin juya halin muslunc a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a yammacin jiya, da ma wasu daga cikin manyan jami’an kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments