Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun ce a shirye suke da su inganta hadin gwiwa da gwamnatin zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.
A wani sako da ya aike, babban kwamandan IRGC Manjo Janar Hossein Salami ya mika sakon taya murna ga Pezeshkian, dan majalisar dokokin kasar Iran, bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugaban kasar Iran a ranar Juma’a.
A matsayinsu na rundunar kare juyin juya hali, ya ce IRGC za ta ci gaba da bin dabarun bayar da hadin kai ga hukumar bisa ayyukanta, da ayyukanta na shari’a da kuma manyan tsare-tsare da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sanar na biyan bukatun kasar.
Ya yaba da irin rawar da al’ummar Iran daga bangarori daban-daban suka taka na fitowa da kuma bin tsari a rumfunan zabe wadanda hakan ya tabbatar gaskiya da kiyaye amana da bin ka’ida a lamarin siyasar kasar, a cewarsa.
Salami ya jaddada cewa, masu kada kuri’a sun sake bada kasa a kan fuskar makiyan juyin juya halin Musulunci tare da dakile munanan makircnsu.
Shugaban na IRGC ya bayyana kwarin guiwar cewa hada karfi da karfe na kasa da kasa zai kai ga nasarar Iran a yakin tattalin arzikin makiya suka kallafa mata.
Ya yi nuni da cewa, ta hanyar dogaro da karfin cikin gida da kuma kiyaye karfin tsarin Musulunci a fagen kasa da kasa wajen maido da cikakken hakkin al’ummar Iran, kasar za ta iya haskakawa a duniya.