Iran ta yi maraba da matakin babban zauren MDD, na neman kwamitin sulhu ya amince da falasdinu a matsayin kasa mamba a majalisar.
Jakadan dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya ce Tehran na maraba da amincewa da kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka na neman sake duba batun shigar Falasdinu a Majalisar.
‘’ shigar da Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya matakin farko ne na magance rashin adalcin tarihi da al’ummar Falasdinu ke fuskanta,” in ji Mr. Iravani a jawabin da ya gabatar a zaman babban zauren Majalisar jiya Juma’a.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince da kuma goyon bayan matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka.
Falasdinu ta cancanci zama cikakiyar memba a Majalisar Dinkin Duniyar.
Mun yi nadama kan yadda Amurka ta kawo cikas ga daftarin sanarwar manema labarai na kwamitin sulhu da Aljeriya ta gabatar, wanda ya bukaci gudanar da bincike na gaskiya da adalci na kasa da kasa don tantance gaskiyar muggan laifukan da aka aikata a Gaza.
Sai dai kuri’ar ta yau ta nuna yadda Amurka ke zama saniyar ware wajen goyon bayan gwamnatin Isra’ila inji jakadan dindindin na Iran a MDD.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da yakinin cewa dole ne a ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da al’ummar Palastinu har sai sun sami damar tabbatar da hakkinsu musamman ‘yancin kai da kuma samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu tare da Quds a matsayin babban birninsa.