Rahotanni sun bayyana cewa jakadan Iran a kasar rasha Kazem Jalili ya fadi cewa batun samar da tsaro ga makamashi na duniya yana kara zama abin koyi ga kasashen dake kudancin duniya, musamman kasashen dake mambobi ne a kungiyar tattalin arziki na Brics domin suna taka rawar da ta dace .
Kazem jalali yayi wannan bayanin ne a jiya Asabar yace matsalolin da ake ciki a yankin, shi ke kawo ci kas da kuma haifar da hauhawan farashi a kasuwannin duniya, da kuma karuwar bukatar da ake da shi a cikin kasashen masu tasowa, ya ce tsaron makamashi ya kasance daya daga cikin ginshikan zaman lafiya na duniya, da kuma ci gaba fiye da kowanne lokaci .
haka zalika Jalili ya kara da cewa kasar iran ba ta kai wa wata kasa hari ba, maimakon haka ma tana kira ne zuwa ga zaman lafiya da tsaro a a kowanne lokaci a duniya.
Jakadan kasar iran ya bayyana cewa a matsayin ta na daya daka cikin mambobin kungiyar tattalin arziki ta Brics dake samar da makamashi iran zata taka muhimmiyar rawa wajen gain an samar da adalaci wajen samar da tsaro da makashi a duniya.