Iran: Jagoran Juyin Juyta Halin Musulunci Ya Umurci Mataimakin Shugaban Kasa Ya Karbi Ragamar Jagorancin Kasa

Jagoran juyin juya haklin Musulunci a nan Iran ya umrci mataimakin shugaban kasa, Muhammad Mukhbir kamar yadda kundinn tsarin mulkin JMI mai lamba 131

 Jagoran juyin juya haklin Musulunci a  nan Iran ya umrci mataimakin shugaban kasa, Muhammad Mukhbir kamar yadda kundinn tsarin mulkin JMI mai lamba 131 ya tanadar a irin wannan halin, ya karbi ragamar jagorancin bangaren zartarwa na JMI. Sannan tare hadinn kai da ma’aikatar sharia da kuma majalisar dokokin kasar a shirya gudanar da zaben shugaban kasa a cikin kwanaki 50 masu zuwa.

A jiya lahadi, 19 ga watan Mayun shekara 2024  ne shugaban kasar Iran Hujjatul Islam Sayyid Ibrahim Ra’isi tare da abokan tafiyan sa, a lokacinda suke kan hanyarsu ta dawowa daga kasar Azarbaijan, inda suka halarci bikin bude madatsar ruwa ta Kiz-Qal’esi sai jirgin da ke dauke da su yayi hatsari, da haka kuma suka kai ga shahada.

Daga cikin wadanda suka yi shahada Tare da shi, akwai Hujjatul Islam, Aali Hashim limamin masallacin jumma’a kuma wakilin jagora a lardin Azarbaijan na gabas. Da kuma ministan harkokin  wajen kasar Hussain  Amir Abdullahiyan Malik Rahmati gwamnan lardin Azarbaijan da Burgadia Mahdi Musawi jami’I mai tsaron shugaban kasa da kuma tawagar masu tukin jirgin shugaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments