Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya yaba da yadda zabubukan kasar suka gudanar cikin nasara, yana mai jinjinawa Al’ummar kasar akan yadda suka ba makiya kunya.
Duk yunkurin rarabar kanuwan jama’ar Iran, yayin da ake tsaka da yakin neman zabubukan da aka gudanar, an yi zabukan cikin nasara da kwanciyar hankali inji jagoran.
A daya bangaren kuma jagoran ya bukaci zababben shugaban kasar akan ya sanya ayyukan al’umma da ci gaba kasar a gaba.