Iran : Isra’ila Ta Kasance Saniyar Ware Fiye Da Kowane Lokaci A A Tsawon Tarihinta

Iran ta yaba da goyon bayan da kasashen duniya ke ba Falasdinu a matsayin mamba a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa matakin ya nuna

Iran ta yaba da goyon bayan da kasashen duniya ke ba Falasdinu a matsayin mamba a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa matakin ya nuna cewa gwamnatin Isra’ila ta kasance saniyar ware fiye da kowane lokaci a tsawon tarihinta na karya.

Nasser Kan’ani ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a ranar Asabar din nan a shafin X, kwana guda bayan da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri da gagarumin rinjaye, inda ya bukaci kwamitin sulhun ya sake duba bukatar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba ta MDD.

Kan’ani ya ce “Gwamnatin sahyoniyawan tana rayuwa ne a cikin wani yanayi da ta zama saniyar ware fiye da kowane lokaci a tsawon tarihinta na karya.

An bar mahukuntan Amurka su kadai suna mara mata baya ko da a cikin al’ummarsu.”inji shi.

Ya kara da cewa: Kuri’ar da kasashen duniya suka yi na nuna goyon bayansu ga cikakken kasancewar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya ya nuna a fili warewar gwamnatin Sahayoniya da Amurka a cikin kasashen duniya.

Kan’ani ya ci gaba da cewa, goyon bayan da jami’an Amurka a fili da boye suke yi ga laifuffukan da Isra’ila ke yi a zirin Gaza “ya zo ne a daidai lokacin da ake goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta a fadin duniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments