Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa wadanda suka goyi bayan Sadam Hussaini a hare haren makamai masu guba kan mutanen garin Sardash na kasar Iran a halin yanzu su suke goyon bayan HKI a kisan kiyashi da kuma amfani da makaman da aka haramta a kan mutanen gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto ministan yana fadar haka a taron tunawa da wadanda hare haren makaman guba wanda shugaban kasar Iraki na lokacin ya cilla a kansu a garin Sardash na lardin Azarbaijan ta gabas a ranar 28 ga watan yunin shekara 1987.
Ministan ya kara da cewa kasar Iran ce kasa ta farko wacce aka yi amfani da makaman da aka haramta amfani da su a yaki bayan boma boman nukliyan da Amurka ta cilla a kan mutanen kasar Japan a shekara 1945.
Yace fiye da mutanen 119 a take, sannan wasu kimani 10,000 suka jikata, wasunsu har yanzun suna jinya a kasar Iran sanadiyyar makaman guna wanda sojojin Sadam Hussain na kasar Iraki a lokacin suka jefa a kan garin Sardash na lardin Azarbaijan ta gabasa. Ya kuma kara da cewa amma kasashen yamma wadanda suka taimakawa Sadan Hussain wajen mallakar wadannan makaman su ne kuma suke hana shigo da magungun don amfanin wadanda makaman suka shafa a kasar iran da dalilai daban daban.
Daga karshe ministan ya bayyana cewa Iran bata neman mallakar makaman kissan kare dangi kuma tana kira ga dukkan kasashen duniya su luzumci wannan dokar, tare da hukuma mai kula da al-amuran makaman guba ta duniya.