Kakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana jinjinawa kasashen duniya wadanda suka bukaci a kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta a taron babban zauren MDD, inda fiye da kasashe 140 suka amince da hakan a yayinda wasu kimani 25 suka ki kada kuri’unsu sannan wasu wadanda basu kai 10 ba, daga ciki har da kasar Amurka suka yi amincewa da bukatar.
Nasser Kan’ani ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Asabar kwana bayan da babban zauren MDD ya zabi bukatar shigar da kasar Falasdinu a Majalisar a matsayin mamba na din din din.
Kakakin ma’aikatara harkokin wajen kasar ta Iran ya kara da cewa a halin yanzun HKI tana kara zama saniyar ware a cikin duniya wannan kuwa duk tare da goyon bayan Amurka da take samu. Ya ce wannan halin zai ci gaba, har zuwa lokacinda zata bace daga doron kasa.
Daga karshe ya bayyana cewa Amurka wacce itace babban kasa wacce take goyon bayan HKI, tana kara zama saniyar ware ita ma.
Kasashe 143 ne suka kada kuri’ar amincewa da Falasdinu cikekkiyar mamba a MDD, a yayinda wasu kasashe 25 suka ki kada kuri’ar kauracewa zaben, sai kuma kasashe 9 daga ciki har da kasar Amurka suka ki amincewa da bukatar.