Gwamnatin JMI da kasat Vetnam sun rattaba hannu kan yarjeniyar aiki tare a bangaren harkokin tsarin cikin gida da kuma yansanda.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS daga Kwala lampa yana bayyana cewa shugaban yansannda na JMI Janar Radan da kuma ministan tsaron cikin gida na kasar Vetnam ne, suka rattaba hannu kan yarjeniyar aiki tare don tabbatar da tsaron cikin gida na kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa aikin tare tsakanin kasashen biyu zasu hada tsaron cikin gida, ayyyukan yansanda, tsaron kasa, yaki da laifukan yanar gizo, digaro da kai da kuma fuskantar takunkuman tattalin arziki na zalunci daga kasashen waje. Har’ila yau da musayar kwarewa a cikin al-amuran tsaro.
Banda haka hadin kan kasashen biyu zai hada da yaki da ayyukan ta’addanci da kuma hana samar da miyagun kwayoyi da kuma yaki da safararsa.
Janar Radan ya je kasar Vetnam ne tare da gayyatar ministan tsaron cikin gida na kasar, kuma ana saran Radan zai gana da ministan harkokin cikin gida na kasar Fommin Chin kafin ya kammala ziyararsa a kasar.