Iran Da Omman Sun Tattauna Kan Al-Amuran Yankin Da Kuma Dangantaka Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da tokwaransa na kasar Omman Badr Al-Busaidi sun tattauna a birnin Muscat babban birnin kasar Omman a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tabo al-amura da suka shafi halin da ake ciki a yankin musamman HKI da kasashen yankin, da kuma dangane da kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Ommam ta taka rawar a zo a gani a kokarin kasar Iran na kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin kasar na makamashin Nukliya.

Ziyarar da Aragchi ya kai Muscat dai yana daga cikin shirin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na tuntubar kasashen makobta daga lokaci zuwa lokaci saboda kara dankon zumunci da su da kuma musayar ra’ayin kan al-amuran da suke faruwa a yankin Asiya ta kudu da kuma duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Omman Badr Al-Busaidi ya godewa Aragchi da wannan ziyarar ya kuma bayyana cewa kasarsa a shirye take ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Asia ta kudu, sannan ya yi kira da a yi amfani da hanyoyin tattaunawa don warware matsalolin da ke tasowa tsakanin kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments