Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sun tabbatar wa China cewa Iran tana da ‘yancin yin amfani da shinfida ikonta kan abin da ta mallaka
Ministan Harkokin Wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana a wani rubutu a dandalin X, cewa:”Ya yi wani taro mai inganci da Wang Yi, Ministan Harkokin Wajen China, a birnin Beijing.”
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tattauna cikakkun bayanai game da ziyararsa zuwa Beijing, babban birnin kasar Sin. A cikin sakonsa a dandalin X, ya ce, “Ya yi wani taro mai inganci da Wang Yi, Ministan Harkokin Wajen China, a Beijing. Kuma bangarorin biyu sun sake tabbatar da ‘yancin Iran na yin amfani da shimfida ikonta kan abin da ta mallaka da kuma kiyaye mutuncin kasarta.”
Araqchi ya kara da cewa: “Sun bayyana wa bangaren China godiyar Iran ga shawarar Beijing mai dauke da matakai hudu, wacce ke da nufin kiyayewa da karfafa tushen tsaro da kwanciyar hankali a yankin.”
Araqchi ya kara da cewa: Iran ta amince da China sosai kuma tana fatan Beijing za ta ci gaba da taka rawa wajen ciyar da zaman lafiya da kawo karshen rikicin da ake ciki, da kuma tallafawa wajen kawo wani sabon tsari bayan yaki da zai tabbatar da daidaito tsakanin bukatun ci gaba da bukatun tsaro.