Iran, China, Rasha za su gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa

Kasashen Iran, Rasha, da China za su gudanar da wani atisayen soja na hadin gwiwa a arewacin Tekun Indiya, a daidai lokacin da ake ci

Kasashen Iran, Rasha, da China za su gudanar da wani atisayen soja na hadin gwiwa a arewacin Tekun Indiya, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Tehran da Washington.

Atisayen, zai kunshi rundunonin sojojin ruwan Iran, da kuma sojojin ruwa daga China da Rasha.

A cewar jami’ai, atisayen yana da nufin inganta tsaron teku da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen.  

Wannan shi ne karo na bakwai da ake gudanar da irin wannan atisayen kuma atisayen ya kunshi ayyuka kamar ayyukan bincike da ceto, tsaron teku.

Atisayen da ke tafe ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke kara barazanar ga Tehran ta hanyar jibge tarin sojoji a kusa da gabar tekun Iran.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tura jiragen sama na da nufin matsa wa Tehran lamba kan tattaunawa, yana mai gargadin cewa rashin cimma yarjejeniya zai kai ga dokar matakin soji “mafi muni” fiye da harin da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliya na Iran a watan Yunin 2025.

Iran ta yi ta musanta barazanar da matsin lambar na Amurka, tana mai dage cewa diflomasiyya ba za ta yi nasara ba bias matsin lamba da barazana ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted