Iran ce kawai ke da izinin cire nakiyoyi daga mashigin Hormuz (Gharibabadi)

Iran ta bayyana cewa ita ce kawai aka ba wa izrinin cire nakiyoyi daga mashigar Hormuz a karkashin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad. Mataimakin Ministan

Iran ta bayyana cewa ita ce kawai aka ba wa izrinin cire nakiyoyi daga mashigar Hormuz a karkashin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran kan Shari’a da Harkokin Ƙasashen Waje Kazem Gharibabadi ya yi watsi da yunkurin Faransa na cewa zata gudanar da wannan aikin a mashigin Hormuz tare da hadin gwiwar kawayenta, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ce za ta gudanar da aikin.    

Mista Gharibabadi ya yi wannan furuci ne bayan da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa da Oman sun yanke shawarar yin aiki tare da abokan hulda, a mashigin Hormuz ba tare da wani sharaɗi ba.

“A ƙarƙashin yarjejeniyar fahimtar Islamabad (MoU), binciken mashigin zai kasance ne kawai ta Iran ba ta wata ƙasa ba,” in ji jami’in na Iran.

A cewarsa Iran ba za ta yarda da wani tsoma baki na ƙasashen waje a cikin cire nakiyoyi daga mashigin Hormuz ba saboda halin da ake ciki a mashigin.

A ƙarƙashin yarjejeniyar mai maki 14, ana buƙatar Iran ta tabbatar da wucewa kyauta ga jiragen ruwa na kasuwanci na tsawon akalla kwanaki 60, tare da dawo da cikakken zirga-zirgar a mashigin Hormuz cikin kwanaki 30.

Iran ta jaddada cewa mashigin ba zai koma yanayin da ake ciki kafin yaƙi ba, tana mai jaddada hakkinta na ikon gudanarwa a mashigin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted