Iran : Ana sa ran mutum miliyan 20 su halarci jana’izar Shahid Ayatollah Khamenei

A Iran an sanar da karin bayanai game da bukukuwan bankwana da jana’izar kwana biyu da aka shirya don girmama Jagoran Juyin Juya Halin Musulinci

A Iran an sanar da karin bayanai game da bukukuwan bankwana da jana’izar kwana biyu da aka shirya don girmama Jagoran Juyin Juya Halin Musulinci na kasar mai rasuwa Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Ana sa ran taron zai jawo hankalin mutane miliyan 20.

Birgediya Janar Hassan Hassan-zadeh, shugaban rundunar tsaro ta juyin juya halin Musulunci ta Tehran (IRGC), wanda kuma shi ne ke jagorantar hedikwatar da ke kula da bukukuwan, ya sanar a lokacin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na kasar cewa an dauki kwararanmatakai domin gudanar da bukukuwan jana’izar cikin tsakani da tsaro.

A cewar Janar Hassan-zadeh, taron da ke tafe zai hada da bukukuwan bankwana, addu’o’in jana’iza, da kuma jerin gwano a ranakun 4 zuwa 5 ga Yuli a Tehran.

A lokacin bikin bankwana na awanni 48, shahararrun masu karatun AlÆ™ur’ani na duniya, masu kasidu na addini, da sauran kungiyoyin al’adu da addini za su shiga cikin shirin.

Don kula da taron jama’a, masu shirya taron sun tsara hanyoyin shiga da fita daban-daban a kan babban masallacin Tehran na.

Da yake jaddada tsarin shirya jana’izar, Janar Hassan-zadeh ya bayyana cewa tsaron jama’a shi ne babban abin da masu shirya taron suka fi mayar da hankali a kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted