Falasdinu ta bukaci duniya ta dauki matakai na zahiri kan Isra’ila

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci al’ummar duniya da su dauki mataki na zahiri don dakatar da ci gaba da mamaye yankunan Falasdinu

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci al’ummar duniya da su dauki mataki na zahiri don dakatar da ci gaba da mamaye yankunan Falasdinu da Isra’ila ke ci gaba da yi.

Riyad Mansour ya shaida wa Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin cewa Isra’ila na kara mamaye yankunan Falasdinu yayin da take wanzar da sojojinta a yankin Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Ya yi gargadin cewa Isra’ila ta kwace iko da kusan kashi 70 cikin 100 na yankin Gaza ba bisa ka’ida ba kuma ta kwace fiye da kashi 60 cikin 100 na Yammacin Kogin Jordan, gami da dukkan yankunan Gabashin Quds da aka mamaye.

A cewar Mansour, wadannan ayyuka ba wai kawai haramtattu ba ne a karkashin dokokin kasa da kasa, har ma sun karya duk wata matsaya da aka cimma,” wadanda duk sun yi watsi da mamaye yankunan.

Ya kuma yi gargadin cewa manufar gwamnatin Tel Aviv shi ne hana duk abu da zai kai ga samar da ‘yancin al’ummar Falasdinawa da kuma kafa kasa mai cin gashin kanta.

Mista Mansour ya kuma yi tir da shirye-shiryen Isra’ila na fadada matsugunai a yankin E1 mai mahimmanci.”

Mansour ya kuma soki Isra’ila saboda lalata matsayin tarihi a wurare masu tsarki na Musulmi da Kirista ta hanyar kutse da aka yi akai-akai yayin da al’ummomin FalasÉ—inawa ke ci gaba da fuskantar rushe gidaje, tilasta musu kaura da hare-hare daga sojojin Isra’ila da mazauna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted