Burkina Faso ta katse huldar diflomatsiyya da Faransa

Gwamnatin Ouagadougou ta sanar cewa ta yanke shawarar katse huldar diflomasiyya da Faransa nan take, kamar yadda wata sanarwa da ofishin firaministan kasar ya fitar

Gwamnatin Ouagadougou ta sanar cewa ta yanke shawarar katse huldar diflomasiyya da Faransa nan take, kamar yadda wata sanarwa da ofishin firaministan kasar ya fitar ta bayyana.

A cewar sanarwar, shawarar ta biyo bayan “binciken da aka yi sosai kan halin da dangantakar kasashen biyu ke ciki a yanzu.”

Gwamnatin ta ce “sharuddan da suka wajaba na kyautata dangantaka bisa girmama juna, da amincewa da juna, da girmama ka’idar rashin tsoma baki a harkokin cikin gida da kuma cikakken ‘yancin kasa duk an shure su ba’a aiki da su.

Tun shekarar 2023 ne Burkina Faso ta kori jakadan Faransa daga kasar, daga baya kuma ta ki amincewa da nadin sabon jami’in diflomasiyya.

A cikin ‘yan shekarun nan, dangantaka tsakanin Faransa da Burkina Faso ta tabarbare sosai saboda rikicin siyasa da tsaro, Wanda ya kai ga Faransa ta janye sojojinta daga kasar, wanda babban koma-baya ne a hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma kokarin faransa na fadada tasirinta a yankin.

A watan Oktoba na 2025, hukumonmin Burkina Faso sun sanar da kama wasu jami’an Turai uku na wata kungiya mai zaman kanta, ciki har da ‘yan kasar Faransa biyu, wadanda ake zargi da leken asiri da cin amanar kasa.

Tun kafin hakan dama kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar, dake kawance a kungiyar AES sun janye daga Kungiyar kasashe da yankuna masu amfani da harshen Faransanci wato (OIF), wani kuduri da ke nuna anniyarsu ta janyewa daga duk wasu Kungiyoyi da ke da alaka da Faransa tare da kira ga sauran kasashen Afirka da su dukufa wajen yada harsunansu na gida, don fitar da kai daga tunanin da masu mulkin mallaka suka kakaba musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted