Araghchi ya isa Bagadaza domin tattauna alakar dake a tsakaninsu

Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Araghchi, ya isa Baghdad, babban birnin Iraki, a safiyar yau Lahadi. An shirya Mista Araghchi zai gana

Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Araghchi, ya isa Baghdad, babban birnin Iraki, a safiyar yau Lahadi.

An shirya Mista Araghchi zai gana da jami’an Iraki domin yin bitar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin da na duniya a yanzu.

A cewar majiyoyin Iraki, ziyarar za ta mayar da hankali kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, biyan basussukan da Tehran ke bin Iraki, tsaron kan iyaka, da kuma dakile kungiyoyin ‘yan ta’adda masu adawa da Iran da ke aiki a kasar Iraki.

Haka zalika bangarorin biyu zasuyi hadin guiwa wajen shirye-shiryen bukukuwan jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei da za’ayi a nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted