Babban hafsan hafsoshin sojojin Kasar Iran Janar Muhammad Bakiri ya bukaci a kafa kwamiti ta musamman don bincike da gano musabbabin hatsarin jirgin fadar shugaban kasa wan
da ya kai ga shahadar Shugaban Ibrahim Ra’isi da tawagarsa.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Janar Bakiri yana fadar haka a yau Litinin. Ya kuma kara da cewa kwamiti mai karfi wanda ya kunshi kwararru ne zasu fayyace musabbabin hatsarin jirgin shugaban kasa wanda ya jawowa kasar asarar shugaban kasa da wasu manya manyan jami’an gwamnati.