Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Abass Araghchi, ya fa wani ran gadin aiki a kasashen Pakistan, Oman da kuma Turkiyya.
Mista Araghchi ya isa birnin Islamabad na Pakistan a ranar Juma’a da yamma.
Ya tattauna da mahukuntan Pakistan kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen, halin da ake ciki a yankin da dai saurensu.
Sabanin yadda wasu kafofin yada labarai suka rawaito Iran ta musanta cewa ziyarar ta Araghchi na da alaka da bukatar da Amurka ta gabatar na Iran ta gaggauta shiga tattaunawa.
Iran ta ce babu wata tattaunawa ta kai tsaye da aka tsara yi tsakanin tawagar Washington da Tehran.
Daga bisani dai shugaban Amurkar ya soke ziyarar da y ace tawagarsa za ta kai a Pakistan domin tattaunawa da Iraniyawa.
Babban makasudin ziyarar shi ne tattaunawa da abokan huldarmu kan batutuwan da suka shafe mu da kuma halin da ake ciki a yankin inji Abass Araghchi a shafinsa na ”X” gabanin ya tashi daga Tehran zuwa Islamabad.
Bayan Pakistan tawagar Iran ta isa kasar Oman inda za ta tattaunawa da mahukuntan kasar kan batutuwa da dama da suka hada da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Haka kuma Abass Araghchi zai isa kasar Rasha duk dai akan batutuwan da suka shafi alaka dama batutuwan da suka shafi kasa da kasa dama yankin baki daya.