Iran: An Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Dan Leken Asirin “Mosad” Mahdi Farid

Mahkunta a Iran sun sanar da zartar da hukuncin kisa akan dan leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila mai suna “Mahdi Farid, wanda ya rika aike

Mahkunta a Iran sun sanar da zartar da hukuncin kisa akan dan leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila mai suna “Mahdi Farid, wanda ya rika aike musu da bayanai akan wurare masu muhimmanci na Iran.

Majiyar shari’a ce ta yi wannan sanarwar bayan da aka yi wa masa shari’a sannan kuma kotun koli ta kasar ta tabbatar da hukuncin akan “Mahdi Farid dan Amanallah, ta hanyar ratayewa.  Shi dai Mahdi Farid ya yi aiki a wata muhimmiyar cibiya, ya kuma sami amincewar kungiyar leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Mosad saboda wurin da yake aikin, inda ya rika aike musu da bayanai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted