Gwamnatin jamhuriyar musulunci ta Iran ta shelanta kwanaki uku na zaman makokin shahadar shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma’ila Haniyyah.
Bangaren hulda da jama’a na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ne su ka sanar da cewa, shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas Isma’ila ya yi shahada da tsakar daren jiya,bayan harin da aka ka kai wa wurin da yake zama a birnin Tehran,haka nan kuma daya daga cikin masu tsaronsa.
Kamfanin dillancin “Irna” yam abaci cewa; Jim kadan bayan sanar da shahadar Mujahdi Isma’ila Haniyyaha ne dai gwmaantin jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar kwanaki na zaman makoki.
Wani sashe na bayanin gwamnatin jamhuriyar msuulunci ta Iran din ya mika sakon juyayin shahadar shugaban kungiyar ta Hamas ga dukkanin al’ummar musulmin duniya da dukkanin masu goyon bayan gwagwarmaya a doron kasa;
Har ila yau wani sashe na sanarwar ya ce; Abinda ya faru wani sabon shafi ne a cikin shafukan manyan laifukan da ‘yan sahahyioniya su ka saba tafkawa.
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta kuma ce,abinda ‘yan sahayoniyar su ka aikata yuana cin karo da dukkanin dokokin kasa da kasa.