An fara yakin neman zaben shugaban kasa a nan kasar Iran har zuwa kwanaki biyu kafin zaben.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a jiya Lahadi ne majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar Iran ta zabi mutane 6 wadanda suka cancanci shiga takarar zaben wanda za’a gudanar a ranar 28 ga watan yunin da muke ciki.
Majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar dai ta zabi mutanen 6 ne a cikin mutane 80 wadanda suka gabatar da takardunsu na neman shugabancin kasar. A ranar 19 ga watan mayun day a gabata ne shugaban kasa marigayi shahida Ibrahim Ra’isi ya rasu a wani hatsarin jingin sama a kan hanyarsa ta dawowa daga kasar Azarbaijan inda ya kaddamar da wata madatsar ruwa wacce kasashen suka gina tare.
Bisa kundin tsarin mulkin JMI dai a cikin kwanaki 50 ne yakamara a zabi sabon shugaban kasa a duk lokacinda shugaban kasa mai ci ya sauka daga mukaminsa ko ya rasu.
Yakin neman zaben dai zai hada da jawabai a gidajen radio da talabijin na kasar, da muhawarori tsakanin yan takara da kuma zagaywa zuwa garuruwa da jihohin don neman kuri’a daga mutane wadanda suka cancanci zabe a kasar.