Iraki Ta Jinjinawa Iran Game Da Goyon Bayan Da Take Bata  

fira ministan kasar iraki ya jinjinawa iran game da gudunmawar da take bata

Rahotanni sun bayyana cewa fira ministan kasar Iraki Ali Al-zaidi ya yaba da irin gudunmawar da iran take bawa alumma da gwamnatin kasar, yace Tehran ta kasance babbar abokiya kasar iraki wajen yaki da ta’addanci

Zaidi yayi wannan bayani ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Iran mohammad baqeer Qalibaf a ziyarar da yakai kasar Iraki , a lokacin ganawar ta su Zaidi ya bayyana irin dangantaka mai zurfi dake tsakani iran da Iraki, kuma yayi kira da a kara karfafa dangantakar  yadda dukkan kasashen biyu za su ci moriyar juna

Ana sa bangaren shugaban majalisar dokokin Iran mohammad Qalibaf ya godewa gwamnatin  Iraqi game da gagarumar rawan da ta taka wajen samun nasara a wajen  taron tattakin Araba’in da aka yi  inda miliyoyin iraniyawa suka ziyarci  wurare masu tsarki na limaman shiriya dake kasar  iraki.

Daga karshe shugaban majalisar dokokin kasar Iraqi ya yi ishara cewa nan ba da jimawa ba sojojin kasar Amurka zasu fice daga Iraki baki daya, sannan yayi kira ga iran da ta sassauta takunkumin da aka sanyawa man kasar iraki a mashigar Hurmuz dake tekun fasha

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted