Kakakin sojan kasar Yemen Janar Yahya Sari ya sanar da cewa a cikin sa’o’I 24 Jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-hare har sau 52 da su ka shafi gundumomin Hudaidah, Ta’iz, Baidha da kuma Sa’adah.
Janar Sari ya ce hare-haren na Saudiyya sun sa an sami shahidaida dama da kuma wadanda su ka jikkata. Haka nan kuma jiragen yakin na Saudiyya sun kai hare-hare akan wasu muhimman cibiyoyi na al’ummar kasar.
Kakakin sojan kasar ta Yemen ya kara cewa Saudiyyar ta yi amfani ne da jiragen yaki samfurin F-15 da Thyphon, kuma sun taso ne daga sansanonin sojan Saudiyya na Khamis Mashit, da garin Ta’aif.
Haka nan kuma Saudiyyar ta yi amfani da makamai masu linzami wadada ta harbo daga gundumar Jizan.
Daga cikin wadanda su ka yi shahada da jikkata da akwai mata da kananan yara da mata,kamar kuma yadda su ka lalata makarantu da gadoji da hanyoyin mota.
Yaki dai ya sake barkewa ne a tsakanin Saudiyya da Yemen bayan gushewar shekaru fiye da 10 da tsagaita wuta, saboda yadda Saudiyya din ba ta yi aiki da wasu sharuddan kawo karshen yakin ba.
Gwamantin Yemen ta San’aa tana son Saudiyya ta dauke takunkumin da ta kakabawa kasar na ruwa da sama wanda yake kara jefa mutanen kasar cikin kuncin rayuwa.
San’aa ta sanar da cewa matukar Saudiyyar ba ta dauke wannan takunkumin ba, to ita ma jiragenta ba za su ratsa ta Ruwan Babal Mandab ba. Haka nan kuma sojojin Yemen din sun sha alwashin mayar da martani ga Saudiyya akan duk wani hari da za ta kai wa kasar Yemen.