Babban kwamandan soji na kasar iran major ganar ali abdullahi ya jinjinawa shugaban kasar iran Masoud pezeshkiya kan jawabin da yayi a gaban babban taron majalisar dinkin duniya a birnin newyork na Amurka, yace jawabin ya isar da sakon alummar iran ga duniya kuma mai gamsarwa
Yace an fassara jawabin a matsayin muryar da ke tashi da karfi ta alummar iran mai alfahari, alummar iran masu daraja sun yi wa shugaban amurka mummunan mari a fuska a idon duniya ta hannun Dr pezeshkiyan
Haka zalika ya fitar da wani gargadi mai karfi a madadin dakarun sojin kasar cewa dakarun kasar za su ci gaba da mayar da martani mai karfi daga duk wani wuce gona da iri har sai sun dauki fansar zubda jinin jagoran juyin musulunci na iran shahid Ayatollah sayyid Ali khamna’I da kuma yara yan makaranta na garin minab dake kudancin kasar iran wanda aka kai musu hari a faron yakin da amurka da isra’la a suka kadddamar kan kasar iran
Acikin jawabin nasa da yayi a majalisar dinkin duniya shugaban kasar iran ya jaddda cewa babu wanda ya isa ya tilasta musu miki wuya, mun tabbatar da cewa ba ma tsoron yaki ko kare kan mu , kuma bama gudun kulla yarjejeniyar zaman lafiya, kuma za mu ci gaba da tsayawa kyam wajen kare kasarmu iran har zuwa karshen numfashi.