AU ta bukaci A kai Zuciya Nesa A Habasha Bayan karbe Filin Jirgi

kungiyar tarayyar afrika ta bukaci a nisanci duk wani matakin da zai kara tada rikici

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna a Habasha da suka kai zuciya nesa, bayan da sabon rikicin ya sake barkewa a yankin Tigray da ke arewacin, inda dakarun TPLF, suka kwace iko da babban filin jirgin sama na birnin Mekelle, hedkwatar yankin.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ne ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu, tare da dakatar da kara rura wutar rikicin.

Ƙungiyar AU ta kuma bukaci a koma kan teburin tattaunawa domin kauce wa sake komawa yakin basasa a arewacin na Habasha.

Rahotanni sun ce an gwabza fada tsakanin dakarun TPLF da sojojin gwamnatin a garuruwan Abala da Erebti, da ke makwabtaka da Tigray a yankin Afar. Wasu majiyoyin tsaro sun ce dakarun TPLF sun karɓe iko da wasu yankuna, yayin da sojojin gwamnatin tarayya ke ja da baya.

Yakin da aka gabza tsakanin mayakan TPLF na yankin Tigray da dakarun gwamnati a shekarar 2020 zuwa 2022 ya yi sanadin mutuwar kusan mutane dubu dari shida, kafin cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Pretoria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted