A daidai lokacin da gwamantin kasar bahrain take ci gaba da daukar mataken murkushe yan shi’a a kasar, gwamman mutane ne suka fito zanga zangar nuna matsayinsu game da ci gaba take hakkokin alumma da gwamnati ke yi musamman ci gaba da tsare manyan malaman shia a gidajen yari a fadin kasar ba tare da yi musu shari’a ba.
Masu zanga zangar sun hau kan tituna ne a kauyen sanabis dake kusa da babban birnin Manama a yammacin jiya laraba, inda suka yi tir da siyasar ci gaba da kama mabiya mazhabar shia musamman malamai masu waazi da kuma takurawa wajen gudanar da ayyukan addini
Watanni da da dama da suka gabata ne jami’an gwamnatin kasar suka dauki matakai masu tsanani wajen murkushe duk wata alama ta addini inda suka kama manyan malaman shia da dama kuma suka sanya tsauraran matakai wajen hana gudanar da abubuwan addini
Ana shi bangaren babban malami a kasar Bahran Ayatulla isa qasem ya nuna damuwarsa matuka game da yanayin da alummar shi’a ke ciki a kasar Baharain ,ya jadddawa cewa cibiyoyin addini a kasar Bahrain suna cikin matsananciyar damuwa game da yanayi da ake ciki.