Iraki Ta Jadda Kin Amincewa Da Duk Wani Kira Na Kulla Alaka Da Isra’ila

Baghdad ta sake nanata kin amincewa da daidaita alaka da Isra’ila a hukumance da kuma a siyasance. Firayim Minista Mohammed Shia al-Sudani ya tabbatar da

Baghdad ta sake nanata kin amincewa da daidaita alaka da Isra’ila a hukumance da kuma a siyasance. Firayim Minista Mohammed Shia al-Sudani ya tabbatar da cewa wannan kalmar  ba ta cikin tsarin siyasar Iraki, yayin da Sakatare Janar na Asa’ib Ahl al-Haq, Sheikh Qais al-Khazali, ya yi kira da a gudanar da bincike kan kalamai da wasu suka yi kan hakan wanda ya sabawa ƙa’idodin ƙasa.

Ofishin Yaɗa Labarai na Firayim Minista ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa al-Sudani ya halarci tarukan Kirsimeti guda biyu da aka gudanar a Cocin Our Lady of Salvation na darikar Katolika da kuma Cocin St. Joseph a Kaldiya da ke  tsakiyar Baghdad. Ya mika sakon taya murna  ga dukkan ‘yan Iraki, musamman Kiristoci, kuma ya bayyana fatansa na cewa Iraki za ta ci gaba da kasancewa a cikin zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma nuna ƙauna tsakanin mutanenta.

A cikin jawabinsa a lokacin tarukan, al-Sudani ya jaddada tushen kasancewar Kiristocin Iraki a matsayin ƙasarsu ce, yana mai jaddada cewa bambancin ra’ayi ginshiƙi ne na ƙarfi da haɗin kai ga al’umma da kuma tushen haɗin kai na asali a Iraki. Sannan ya sake nanata cewa daidaita alaka da Isra’ila ba abu ne da za a amince da shi a Iraki ba.

Ya kara da cewa ɗabi’un da Yesu Almasihu ya kawo da kuma waɗanda saƙon Musulunci sun ƙara haɓaka wani babban gishiki  da ke kare tsarin zamantakewa, yana mai jaddada alƙawarin kiyaye alamun haɗin kai da kuma zaman lafiya ta hanyar hadin gwiwa tsakanin majami’u da masallatai, waɗanda ya bayyana a matsayin wuraren amince da kauna da kusanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted