Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi watsi da daukaka karar da Isra’ila ta shigar kan sammacin da ta fitar a baya na kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant. .
A watan Nuwamba ne, kotun ta fitar da sammacin bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Sammacin ya fusata Isra’ila da Amurka, wadanda tun daga lokacin suka kakabawa manyan jami’an ICC din takunkumi.
Benjamin Netanyahu ya kira matakin a matsayin “mai nuna kyama ga Yahudawa.”.”
A cikin watan Mayu, Isra’ila ta bukaci kotun ta ICC da ta yi watsi da sammacin.
Kotun dai ta yi watsi da bukatar ne a ranar 16 ga watan Yuli.
Mako guda bayan haka Isra’ila ta nemi izinin daukaka kara kan hukuncin, amma alkalan kotun sun yanke hukunci a ranar Juma’a cewa “batun kamar yadda Isra’ila ta tsara, ba za a daukaka kara ba.”
“Saboda haka majalisar ta ki amincewa da bukatar,” in ji kotun ta ICC